Da Dumi-Dumi

Mai Rose Ya zama gwarzon shekara

blogger@northflix.ng 2020-02-11 05:00:51 Labarai


Matashin jarumi a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Amir Iliyasu Mai Rose, ya zama gwarzon shekarar 2019 wanda kungiyar  Kanon Dabo  Media ta karrama shi a matsayin gwarzon shekarar bara a bangaren mai bada umarni.
Kungiyar ta karrama Amir Mai Rose ne, a taron da ta gabatar na karshen shekara a ranar 25 ga watan Janairun da ya gabata.
A lokacin da wakilin mu ya ke zantawa da shi dangane da karramawar da a ka yi masa cewa ya yi.
"To ni dai babu abun da zan ce sai dai na yi godiya ga Allah, bisa wannan karramawar da a ka yi min, ko babu komai wannan abun alfahari ne a gare ni yadda na zama har wasu daga nesa sun kalli aiki na har su ka ga da cewar su karrama ni, wannan ai abun alfahari ne a gare ni.
Ya kara da cewa "Tsawon shekaru da na shafe ina harkar fim an ba ni lambobin karramawa da dama amma wannan ya fi daukar hankali na, domin kuwa a baya ina shiga gasa ne, wata gasar ma har sai na biya kudi a karrama ni. To amma a wannan kawai sun kai min takardar gayyatar za su yi taro kuma ina daga cikin mutanen da za su karrama, to ka ga akwai bambanci da karramawar da kai ka je ka nema da kuma wanda ba kai ne ka nema ba, kawai kallon nagartar aikin ka a ke yi kuma aka ba ka, domin haka ina godiya ga Allah da ya kai ni ga wannan mataki, kuma ina godiya ga wannan kungiyar da ta ba ni wannan Kambun na karramawa”. Inji Mai Rose.
Shi dai Amir Iliyasu Mai Ross, mai bada umarni, mashiryi kuma jarumi ne, a masana’antar Kannywood na tsawon shekaru kusan 20. Shi ne mashiryin fim din Asusun Ibro da Jarin Ibro da kuma wasu fina-finan da su ka fito a shekarar 20002, kuma daga wakar fim din Jarin Ibro, ta Baba sai mini mai Rose ya samu lakabin Amir Mai Rose.

Labarai masu kamanceceniya