Da Dumi-Dumi

Ban daina shirin Dadin Kowa ba -Umar Sani Jigirya (Sallau)

blogger@northflix.ng 2020-02-12 09:22:40 Labarai

Umar Muhammad Sani Jigirya wanda a ka fi sa ni da suna Sallau a cikin shirin Dadin Kowa na tashar Arewa 24, kuma ya na daga cikin fitattun jaruman da suka haskaka shirin na Dadin Kowa wanda ya yi suna a idon duniya, kuma ya na cikin wadanda suka fara shirin har kusan zuwa zango na uku a na tafiya da shi.

Yanzu haka dai jarumin yakan dade a gefe ba tare da anji duriyar sa ba, sakamakon yanayin yadda shirin ya sauya salo wanda wasu ke ganin kamar ya ja baya da harkar. A kan wannan batun ne jaridar mu ta Northflix ta tuntubi Salau kowa na ka, dangane da irin rawar da ya ke takawa a cikin shirin tun daga farko har zuwa wannan lokacin, inda ya fara da cewa:

"Tun da farko an fara shirin da ni ne tun daga Dadin Kowa, a ka zo Sabon Salo, yanzu kuma a ka shiga wasa farin girki. A yanzu matsayin da na ke ciki a wasa farin girki shi ne, an kira ni na sanya hannu a kan aikin, ka ga wannan ya tabbatar da ina ciki shirin kenan”. Inji jarumin

Ta bangaren Gwagwarmaya ko ta ya a ka fara?

"To gwagwarmaya dai ga duk wanda ya ke kallon mu ya san ta inda a ka faro, domin an fara ne tun daga babu Sallau, har a ka zo a ka samar da shi, har a ka zo a ka yi tunanin a ajiye Sallau, har a ka zo a ka dawo da Sallau, kuma har a ka yi tunanin bayan an dawo da shi din a kara ajiye shi, sannan a ka kara yin tunanin a kara dorawa da shi. To amma dai ni irin kallon da na ke yi wa lamarin, ba shi mutane su ke yi masa ba, domin ni a yadda na ke kallon al'amarin, wani abu ne da idan ka kula, sun kindimo abun ne ya fi karfin yadda su ke tsammani, kusan gidaje sun yi yawa a Dadin Kowa kuma mutane sun yi yawa, domin haka yaushe a ka yi labarin wane da wane? To ba a dakko abun yadda zai iya karewa ba, kuma ba a dakko abun yadda za a tsaya a yi ta labarin wani ba, wannan ta sa dole sai dai a bi abun a hankali ". inji Salau.

Dangane da yadda mu'amalan sa ke kasancewa a bayan fage a matsayin sa na Umar Muhammad Sani Jigirya, cewa ya yi.

"To a bayan fage Alhamdulillahi, domin gwagwarmaya da na yi ta kasance, ina yin 'yan wasanni na, har a na gayyata ta wurare, domin na je na nishantar da mutane, sannan kuma ina yin harkokina na aikin gidan rediyo har yanzu ina yi ban daina ba, kuma ina zuwa garuruwa domin na gabatar da shirye-shirye na, kuma akwai harkokina na kasuwanci ina yi, kuma har da harkar siyasa ina yi duk da sauran abubuwa dai da na ke yi ina nan ina yi ban fasa ba, saboda na debo harkokin nawa da yawa nima ".

Amma har yanzu abun da mutane su ke kallo, shi ne ka kasa bambanta kan ka da matsayin ka na Sallau a shirin Dadin Kowa, da kuma sunan ka na Umar Sani Jigirya.

"To, ba kasa cire kaina na yi ba, domin idan ka kula a yanzu muna zaune da kai ne muna yin hira a matsayina na Umar Sani Jigirya, ka ga in da Sallau ne ba za ka zauna da shi ba, domin haka ko a yanzu ma ai an samu bambanci, kuma yadda na ke mu'amala ta ina yi ne a matsayina na Umar Jigirya , domin haka mu'amalar Sallau ta na faruwa ne a cikin shirin Dadin Kowa, kuma mu'amalar Umar Sani Jigirya, mai kyau ce, kai da kan ka yanzu ka gani yadda jama'a su ke zuwa mu yi managa da su, wannan ya zo idan ya tafi ma wani ya zo, to haka mu'amalata ta ke kasancewa a tsakanin jama'a mata da maza, domin abun mamaki za ka ga mutane daga wasu kasashe kamar Benin, Chadi, Togo da kuma sauran kasashe duk a na kira na, kuma su na bibiya ta ta shafin Instagram dina da dai sauran shafukan da na ke da su. Kuma wani abun alfahari sai ka je waje ka ga wani babban mutum ya kira sunan ka wanda kai ba ka ma san shi ba, to ina alfahari da wannan irin baiwa da Allah ya yi min". A cewar Sallau.

DAGA karshe ya yi fatan alheri ga masoyan sa saboda kaunar da su ke nuna masa.

Labarai masu kamanceceniya