Da Dumi-Dumi

Rashin fahimta ne ya sa a ke kallon mu baibai -Sadiq Sani Sadiq

blogger@northflix.ng 2020-02-13 10:44:12 Labarai

 

Jarumin fina-finan Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya bayyana Kannywood a matsayin wuri mai tsafta kuma mai dauke da mutane masu tsoron Allah a cikin  masana'antar.

Jarumin ya fadi haka ne a wata tattauna da wata kafar sadarwa ta mujallar Sirrin su ta yi da shi, sakamakon wani bawan Allah da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta ya na cewar, Sadiq Sani Sadiq ya je Maiduguri, kuma kullum sahun sallah ba ya wuce shi.

Wannan dalilin ne ya sa a ke tambayar Sani Sadiq din cewar, ya na ganin mai rubutun ya dauki ‘yan fim a matsayin bata gari kenan?

Sai ya fara da cewar" Duk cikin al’umma dole akwai mutanen kirki akwai kuma bata gari, illa dai kawai wasu mutane marasa dogon tunani kuma marasa fahimta suna yiwa ‘yan fim kallon mutanen da ba mutanen kirki ba, amma duk mutumin da yake da dogon tunani yasan me yake yi, kuma duk mai ilimi na addini da na boko yasan cewa ‘yan fim ba mutane ne marasa kirki da tarbiya ba, illa kawai dai wasu tsirarun mutane wadanda basu fahimci inda muka dosa ba, ke yi wa abun wani kallo na daban. Kuma sadaukarwa addu’ar iyaye ita take bin mu, sai mu ce Alhamdulillahi, domin muna kwatanta gaskiya da rikon amana tare da son mutane, wannan dalilin ne ya sa muke samun cigaba har mu ka zo inda muke a halin yanzu".

Jarumin ya kara da cewar" Kuma shi girman kai da ka ke gani ba karamar illa ce da shi ba, mutum inda har yasan abun da yake yi, to yakamata ya gane cewar shi masoyi ba abun wulakantawa ba ne, ko da kuwa ya ya mutum yake domin dan Adam ya na da daraja ko ina yake". A cewar Sadiq Sani Sadiq.

Labarai masu kamanceceniya