Kannywood masana’anta ce ba dandalin wasa ko nishadi ba ce- Adamu kwabon masoy

blogger@northflix.ng 2020-02-11 02:08:50 Labarai

Malam Adamu Muhammad Kwabon Masoyi, ya bayyana masana'antar a matsayin wadda ta ke kunshe da karancin tarbiyya da kuma rashin ganin girman na gaba a cikin ta.

Malam Adamu Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da su ke tattaunawa da wakilin mu dangane da masana'antar kasancewar sa Dattijo kuma Uba a cikin ta.

A cewar sa “Ita harkar fim a matsayin ta na masana'anta, ta samar da dumbin ayyukan yi ga matasa wanda kuma hakan wani ci gaba ne da a ka samu, amma babbar matsalar harkar a yanzu ita ce karancin tarbiyyar yaran, domin sau da yawa za ka je waje sai ka ga ba a ma damu da zuwan ka ba, kuma ba a san kai wani ne ba a ciki. Amma dai duk da haka ni a matsayina na Adamu Muhammad zan iya cewa ba ni da matsala da kowa sai dai wadda ta shafi harkar baki daya, domin haka, kiran da zan yi shi ne su sa hankali a cikin aikin su, su cire kyashi da hassada, su rinka taimakon junan su, domin hassada da kyashi ne ya ke kawo fadace-fadace da tozarta juna, ta yadda har a ka samu kai a halin da a ke ciki a yanzu ". inji Kwabon Masoyi.

Ya kara da cewar “Harkar fim sana' a ce domin haka su daina daukar ta da wasa, kamar yadda su ke yi mata a yanzu, saboda su na daukar sana’ar a matsayin wasa ko wani dandalin nishadi, kuma su rinka kiyayewa da kuma girmama juna, domin duk harkar da za ka ci ka sha ka yi wa kan ka sutura to bai kamata ka dauke ta da wasa ba, domin haka a rinka kiyaye mutuncin mu da na ita kanta sana'ar ta mu, domin gujewa abun da mutane za su rinka ganin an yi abun da bai dace ba". A cewar Kwabon Masoyi

Labarai masu kamanceceniya