Wa zai maye gurbin Naziru Sarkin wakar San Kano?

blogger@northflix.ng 2020-03-19 04:04:45 Labarai

 

Fitaccen mawakin sarautar nan mai suna Naziru M Ahmad wanda a ke yi wa lakabi da Sarkin wakar Sarkin Kano ya yi murabus daga mukamin sa.

Mawakin ya rubuta takardar yin murabus din ne a ranar Juma'ar da ta gabata, 13 ga wannan watan na Maris.

Mai martaba tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi Lamido na II wanda ya nada Naziru M Ahmad a matsayin Sarkin wakar Sarkin Kano a ranar 27 ga watan Disamba na shekarar 2018.

Murabus din Naziru baya rasa nasaba da tube wanda ya yi masa sarautar, Malam Muhammadu Sanusi, wanda gwamnatin jihar Kano ta sauke shi daga mukamin sa a kwanakin baya. Tsohon Sarkin wakar Sarkin Kano, ya kwashe kwanaki 435 ya na sarautar sa.

Tun kafin Malam Muhammadu Sanusi Lamido na II ya zama Sarkin Kano, Naziru ya na daya daga cikin mawakan sa da suka dade tare da shi.

Bayan murabus din na Naziru, sai kuma kallo ya koma sama wurin ganin mawakin da zai maye gurbin sauratar Naziru a yanzu haka.

A wani hasashen da a ke yi an gano cewa sarautar ba za ta wuce tsakanin mawaka guda biyu ba, ko dai Aminu Ladan Abubakar (Alan Waka) ko kuma Dauda Kahutu Rarara. Dukkanin mawakan dai kowa ya baje kolin basirar sa a wurin sabuwar wakar taya sabon Sarkin murnar nadin sarautar Kano da a ka yi masa. Kamar yadda su ka yi masa a lokacin da ya na Sarkin Bichi.

Mawakan biyun dai sun kasance dukkanin su mawaka ne ga sabon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero. In dai ba a manta ba, a ranar 13 ga watan Agusta na shekarar 2019 ne dai mai martaba Aminu Ado Bayero, a lokacin ya na Sarkin Bichi, ya yi  bikin nada Alan Waka a matsayin Dan Amanar Bichi. Wanda kuma shi ne nadin Sarauta ta farko da Sarkin na Bichi ya yi masa tun bayan lokacin da gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin na sa a matsayin Sarkin na Bichi kafin ya zama Sarkin Kano a yanzu.

Ya zuwa yanzu dai, ba a iya sanin wanda zai maye gurin tsohon Sarkin wakar Sarkin Kano, Naziru M Ahmad.

Labarai masu kamanceceniya