Kotu ta gayyaci Baban Chinedu sakamakon kage da Afakallah ya ce ya yi masa

blogger@northflix.ng 2020-03-21 14:22:52 Labarai

Kotun shari'ar musulunci da ke zaman ta a filin Hockey unguwar Hausawa a Kano, ta fara sauraron karar da Isma'il Na'abba Afakallahu ya shigar a gaban ta, sakamakon maganganun da Haruna Yusuf wanda a ka fi sa ni da Baban Chinedu ya yi a shafin sa na sada zumunta na Instagram, cewa ya cinye kudin marayu na diyar marigayi Rabilu Musa Dan Ibro wanda gwamnatin Kano ta bayar ta hannun sa domin a siye mata kayan daki.

Sakamakon wannan zargin ne Afakallah ya garzaya zuwa kotun domin neman a fito da gaskiyar maganar da shi Baban Chinedu ya yi a kansa.

Bayan da kotun ta fara saurar korafin da mai kara ya shigar a gaban ta, sai ta saka ranar 1 ga watan 4 na shekarar 2020 domin fara sauraren shari'ar.

Tuni kuma kotun, ta turawa Baban Chinedu takardar gayyata zuwa ofishin sa dake Kano, domin ya zo ya yi mata jawabi dangane da korafin da a ka shigar a kan sa.

Labarai masu kamanceceniya