Za mu yi gajeran hoton bidiyo na fadakarwa a kan cutar Corona -Aminu S Bono

[email protected] 2020-03-21 05:59:18 Labarai

 

Fitaccen mai bada umarni a fina-finan Kannywood, Aminu S Bono, ya shaidawa majiyar mu yunkurin sa na son haduwa da jarumai da ma wasu da yawa daga cikin ‘yan Kannywood domin hada wani hoton bidiyo na fadakarwa tare da wayar da kan al’umma dangane da sabuwar cutar Corona virus wadda a ke kiranta da Covid-19 mai sarkake numfashi.

Aminu S Bono, ya shaida mana hakan ne a yayin tattaunawa da mu ka yi da shi dangane da yunkurin da Kannywood take domin wayar da mutane duba da yadda kowa cikin sa ya duri ruwa game da bullowar cutar wanda manyan kasashen duniya suka tsorata da ita.

Akwai wani yunkuri da Kannywood ta ke domin wayar da kan al’umma dangane da wannan cuta da a ke fama da ita a kasashen duniya?

Sai ya ce “Idan ma akwai gaskiya ni bai karaso waje na ba tukun, sai dai nasan da cewa da yawa daga cikin mu suna yin gajeran sako na bidiyo su na yadawa a kafafan sadarwa su na fadakar da al’umma, amma gaskiya babu wani aiki da a ke kokarin yi a kungiyan ce”.

Amma baka ganin ya kamata Kannywood ta yi wani yunkuri, domin wayarwa da mutane kai duba da cewa duk wani sako da a ke son turawa yafi tafiya cikin hanzari idan daga bangaren Kannywood ya bulla?

“Gaskiya ne wannan kuma ni ma a kan kai na ina tunanin hakan, sannan kuma Ina kokarin hada hakan mu baki daya mu yi gajeran sakon bidiyo da  jarumai maza da mata mu yi fadakarwa a kai domin mu wayar da kan al’umma, musamman na cikin karkara wadanda basu san yadda za su yi su kare kan su ba”.

Amma a ganin ka me ya sa gwamnati ba ta amfani da masana’antar Kannywood domin wayar da kan al’umma ko tura wani sako wanda a ke son ya yi gaggawar zuwa duk da cewar sakon na masana’antar ya fi saurin yaduwa?

“Eh to wannan gaskiya gwamnati ba ta mayar da hankali wajen neman Kannywood ta yi mata irin wannan aikin, mafi akasari idan hakan ya taso tafi neman ‘yan Kudu wanda kuma sakon da su ke son turawa baya yin nisa a Arewacin kasar nan, in dai a ka ce ‘yan Kudu ne za su isar da shi, dalili kuwa shi ne mutanen mu na kauye da karkara ba su san jaruman Kudancin kasar nan ba, wasu  ba jin turanci su ke yi ba, domin haka ba sauraran su a ke yi ba, kin ga kuwa duk wani sako da za su isar ba ya zuwa kenan, wannan rashin isar da sakon, sai ki ga idan wata baraka ya ta shi tasowa daga can za ta bullo, saboda ba su san ta yadda za su kare kan su ba. Mu kuma gwamnati a duk lokacin da za ta bukace mu shi ne lokacin siyasa, mu kuma a nan ba za mu je mu tallata su biya mu ba a bangaren mu, kuma ina ganin mu muka bada kofa ga wannan matsalar, domin mun nuna aikin kudi mu ke so mu yi a biya mu. Wanda ba haka rayuwa take ba, akwai abubuwa da dama da mutum zai bigi kirji ya yi badan kudi ba sai domin sadaukarwa, misali wannan matsalar ta cutar Corona Virus, ba sai mun jira gwamnati ta bamu kwangilar yin hakan ba, a kankin kan mu ya kamata mu hada kungiya mu wayarwa da mutane kai na birni da na karkara ko ba komai mu kan mu za mu kare kan mu“. A cewar Aminu S Bono.

 

Akwai wani tsari da a ke kokarin fito da shi na tattara bayanan jarumai dama duk wani da ya ke karkashin masana’antar Kannywood, me za ka ce game da wannan?

“Tsarin na data base ci gaba ne sosai ga masana’antar Kannywood, domin kamar an kara sabanta masana’antar ne, misali yanzu wani a kasar Russia, Amurka da ma sauran kasashen duniya ya na son tallata wani abu na sa kuma ya na bukatar ya yi amfani da wani jarumi ko jaruma ko wani dai a masana’antar ba sai ya tsaya kame -kame ba, kawai shiga zai yi ya ne mi sunan  mutum a internet ya ga waye shi, karatun sa, shekarun sa da kuma cancantar sa, kin ga ai sauki kenan ya zo. Bayan nan ko a ina ka ke duniya za ta san da zaman mutum da matsayin sa dan wane masa’anta ne, kin ga kenan ci gaba a ka samu wanda dama a ke fatan samu, kuma mu na sa ran bullowar wasu hanyoyin na ci gaba a masana’antar Kannywood”.

Idan na fahimce ka tsarin data base ci gaba ne a masana’antar kannywood kenan?

“Kwarai kuwa, dari bisa dari, domin ko kadan ba shi da matsala, kin ga muna goyon baya a kai kenan”. Inji Aminu S Bono

Labarai masu kamanceceniya