Garzali miko ya zama cikakken dan fim

blogger@northflix.ng 2020-03-21 06:30:55 Labarai

 

 

A Yau Juma'a 20 ga watan 3 shekarar 2020 ne fitatcen jarumi kuma mawaki garzali miko ya zaryarci ofishin shugaban Hukumar tace finafinai da dab'i reshen jihar Kano Ismail Na Abba Afakallahu tare da mataimakin shugaban Kungiyar MOPPAN Alh Sani Sule Katsina.

Kamar yadda shugaban Kungiyar ya wallafa a shafin sa na Instagram ya rubuta cewa makasudun ziyarar da jarumin yayi shi ne yazo ya amshi Form na kasancewarsa cikakken dan fim ma'ana cikakken jarumi wanda zai bashi damar cigaba da ayyukan shi bisa tsarin Doka anan jihar Kano.

Bayan jarumin ya guji jihar Kano dan kin bin doka da kuma kin bin tsarin da kungiya tayi A baya, Amma yanzu ya dawo bayan tantanceshi da zaayi ya kuma cike form zai samu damar mallakar katin shaidar da zai bashi damar gudanar da ayyukansa a lungu da sako na jihar kano cikin kaida da doa ba tare tare da tsangwama ba. Inji shugaban Kungiyar Isma'il Na'Abba Afakallahu

Labarai masu kamanceceniya