Ali Nuhu, Maishadda da Hassan Giggs za su je gwajin COVID-19 a Kano

blogger@northflix.ng 2020-03-25 09:33:02 Labarai

 

 

Sakamakon bayanai da su ka fito daga hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya wanda gwamnatin Jihar Legas ta bayyana cewa Ali Nuhu da wasu 'yan Kannywood biyar wadan da su ka hada da Hassan Giggs, Abubakar Maishadda da Ado Gwanja na bukatar zuwa gwajin cutar Corona Virus sakamakon halartar taron nan na AMVCA da a ka gudanar mako biyu da su ka shude a garin Legas.

Gwamnatin jihar ta Legas ta yi kira ga duk wanda ya halarci bikin da ya je a yi masa gwajin Corona Virus saboda ta gano cewa wani mai dauke da cutar ya halarci bikin, kuma dole ya yi cudanya da mutane da dama a wajen taron wadan da ba za a iya tantancewa ba.

A bayyanan da mu ka samu daga bakin jaruman, sun nuna tawakkali ga wannan ibtila’i da neman addu’ar Allah ya kare su da dukkanin ‘yan Nijeria da ragowar sassan duniya da wannan annoba ta ritsa da su. Kuma a yau za su je gwajin wannan cuta domin sanin halin da su ke ciki.

Cutar COVID-19 dai ta zama ruwan dare gama duniya wadda a halin yanzu ta halaka dubunnan mutane a sassa daban-daban na duniya, a ciki har da Nijeria inda a kalla mutane 42 ne a ka tabbatar sun kamu a ciki har da manyan jami’an gwamnatin tarayya, da gwamnonin jihohi guda biyu da kuma ‘ya’yan attajirai.

Cutar COVID-19 wadda ke nufin CORONA VIRUS DISEASE 2019 ta samo asali ne daga kasar Sin (China) a wani gari mai suna Wuhan, amma yanzu ta fantsama a duniya. Cutar na toshe hanyoyin numfashi ne har mutum ya halaka idan bai samu kulawar gaggawa ba.

Kasashen da cutar ta fi yiwa illa sun hada da Italiya, Ingila, Amurka, Faransa, Jamus, Iran, da kuma koriya ta Kudu.

Labarai masu kamanceceniya