Da Dumi-Dumi

Covid-19: An dakatar da yin fim saboda Corona -MOPPAN

blogger@northflix.ng 2020-03-26 06:02:57 Labarai

 

Sakamakon halin da duniya ta tsinci kan ta na annobar cutar Covid-19, ya sanya kungiyar kwararru ta masu shirya fim ta kasa MOPPAN ta fitar da wata sanarwa a safiyar ranar laraba 25 ga watan Maris, wadda ta ke dauke da umarnin dakatar da duk wani aiki da ya shafi sana'ar gudanar da harkar fim a masana'antar fina-finai ta Kannywood a dukkanin fadin kasar nan har zuwa nan da kwanaki 30.

Sanarwar mai dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na kungiyar, Al-Amin Chiroma, ta rawaito cewa shugaban kungiyar, Dakta Ahmad Sarari, ya umarci dukkanin 'yan kungiyar da su bi umarnin gwamnati wajen kauracewa taruwa a wuraren da a ka hana ko wani aiki na fim da zai kawo jama'a a wurin.

Sanarwar ta kuma umarci 'yan kungiyar da su rufe wajen sana'ar su, domin dakile yaduwar cutar kamar yadda ta ke bazuwa kamar wutar daji, sannan duk wanda ya karya doka zai hadu da fushin hukumar.

Domin haka ne kungiyar ta yi kira ga mambobin ta da su zauna a gida tare da killace kan su, yayin da idan mutum ya ji yanayin da bai gamsu da shi ba, ya sanar da masu kula da wannan cutar da a ka tanadar domin tabbatar da irin halin da ya ke ciki.

Kungiyar ta MOPPAN ta yi fatan Allah ya kawo mana karshen wannan musifa da mu ka shiga ta Covid-19.

Labarai masu kamanceceniya