Da Dumi-Dumi

Abun da ya bamban ta ni da sauran jarumai -Mu'azu Boshkiddo.

blogger@northflix.ng 2020-04-02 05:22:10 Labarai


Fitaccen jarumin barkwanci wanda ya fi shahara a gajerun fina-finai a Soshiyal Midiya, Muhammad Mu'azu Boshkiddo, ya bayyana irin Salo da kuma tsarin da ya bamban ta shi da sauran jarumai na masana'antar fina-finai ta Kannywood wanda hakan ya sa ya shara a cikin harkokin fina-finan na barkwanci har ya zama wani babban jarumi.
Boshkiddo ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu dangane da yadda a ke ganin sa na daban a cikin harkar fim.
Tun da farko ya bayyana yadda ya samu kan sa a cikin harkar inda ya fara da cewa.
"To gaskiya harka ta ta fim musamman wanda a ka fi sa ni na, na fara ta ne da wasa, saboda ni yanayi na mai barkwanci ne, domin haka idan mu na tare da abokai na za ka ga a na ta wasa da dariya, domin ko a lokacin da ina sakandire, idan ban je ba za ka ga a na tambaya ko Lafiya ban je ba, saboda in ba na nan ba hayaniya da wasa da dariya, saboda haka idan ba na nan a na ganewa. Haka ma da na shiga Jami'a a ke yi. To irin wasan da mu ke yi na barkwanci ya sa na yi tunanin ya ya za mu yi mu fito da shi duniya ta gani, domin haka sai mu ka fara yin sa mu na sakawa a waya mu ke turawa a Internet, mutane su na gani daga nan sai Allah ya fadada abun ya kai har gidajen TV, ya kai ma in da ba ma tunani".
Dangane da manufar da ya ke so ya isar kuwa cewa ya yi.
"Kishin Hausa da al'adun ta ya sa na fi bada karfi a kan wannan wasan na barkwanci, shi ya sa ma za ka ga ba ma yin na turanci, ba kuma don ba mu iya turancin ba ne, sai don kawai mu na son mu raya yaren mu na Hausa, domin haka idan mu ka yi da yaren mu na Hausa, a kasa sai mu rubutu da turanci, saboda wadanda ba sa jin Hausa idan sun gani su gane”.
Ko me Boshkiddo ya fi mayar da hankali wajen isar da sakon sa?
"Mu abun da mu ka fi mayar da hankali a kan sa shi ne, mu na dubawa mu ga me ya ke faruwa a lokacin? Gwamnati ce ta ke so ta yada wani abu a gari, ko kuma wani abu a ka yi na ban dariya. To duk wani abu dai da ya ke tashe a lokacin shi mu ke dubawa mu yada wa mutane, domin haka muna isar da sako ne ga jama'a a kan abun da ya ke faruwa cikin barkwanci".
Ko me ya bamban ta ku da sauran jarumai na masana'antar fina-finai ta Kannywood?
“To mu da su bambanci ba yawa, domin mu da su duk jarumai ne, duk ajin mu daya, amma a wajen da mu ka bambanta da su shi ne, mu ne mu ke yin komai da kan mu, kamar yanzu za mu iya haduwa mu kira su mu yi aiki tare, mu ke komai da kan mu, mu tsara labarin, mu shirya, mu bada Umarni, wannan shi ne bamabancin mu da su kawai". A cewar Bushkiddo
Jarumin ya yi kira ga jama'a da su rinka kallon shirye-shiryen na su cikin nutsuwa, domin fahimtar yadda sakon ya ke da kuma irin darasin da ya ke dauke da shi.

Labarai masu kamanceceniya