Da Dumi-Dumi

Makiya ne su ka kitsa cewa muna dauke da Coronavirus -Mai Shadda

blogger@northflix.ng 2020-04-02 09:17:20 Labarai

Ma shiryin fina-finan Hausa a masa’antar Kannywood, Abubakar Bashir Mai Shadda ya ce makiya ne su ka kitsa cewa shi da abokanan sa sun kamu da cutar Coronavirus. Abubakar Bashir Mai Shadda ya bayyana wa majiyar mu yayin zantawa da shi game da maganganun da a ke ta yadawa cewa ya samu cutar. Wannan dalilin ya sa majiyar mu ta tuntube shi domin jin game da wannan batu, inda mu ka fara tambayar sa kamar haka. Mu na son jin ta bakin ka a bangaren mu dangane da wannan zargi da wasu ke yi maka me ne ne gaskiyar lamarin? Maishadda ya ce “Gaskiya babu wannan magana, ina nufin ni da abokan aiki na bamu dauki wannan cuta ta covid-19, abun da yake faruwa shi ne wannan labarin na Corona shiryayyen labari ne wanda ba shi da sahihanci, saboda taro ne mu ka je jihar Legas, kuma a kalla mun yi sati biyu da dawowa, domin a ranar da a ka ce muje a yi mana gwaji kwanan mu goma sha biyu bayan mun dawo, kuma wanda a ke zargin ya na dauke da cutar a can wajen taron shi ma karya a ke masa, domin haka wannan duk wasu labarai ne na kanzon kurege”. Amma wane matsayi masana’antar Kannywood take ciki a yanzu sakamakon dakatawa da a ka yi da aiki saboda wannan annoba ta covid-19? “To alhamdulillahi mu na godiya ga Allah a duk halin da mu ka tsinci kan mu, harkar fim yanzu ba ma a iya masana’antar Kannywood ba, duk masana’antun fina-finai sun samu matsalar nan, domin duk fina-finai da za a haska a sinimomi sun tsaya cak, sannan kuma mun dakatar da shirya wasu fina-finai da ya kamata a ce mun kamala su a yanzu, sakamakon halin da a ke ciki, wannan kuma shi ne kadai abun da zai dan taba masana’antar bama ita kadai ba , duk wata masana’anta ta harkar fim da a wannan shekara da muke fatan mikewar kasuwancin wannan masana’anta. Zamu iya cewa sai dai Allah ya kawo karshen wannan annobar ta Covid-19, Sai dai mun yarda duk wani abu da zai zo daga Allah ya ke kuma shi ya ke kawo tsanani sannan ya ke kawo sauki, domin haka mu na sa ran zai zama labari insha Allahu, Coronavirus zai zama labari ta zama tarihi ya wuce. Sannan mu na fatan masoyan mu su kasance damu su ci gaba da bibiyar mu kuma insha Allah da an gama hutun nan na Corona zamu ci gaba da haska musu fina-finai tare da nishadantar dasu“. A cewar Abubakar Bashir MAISHADDA.

Labarai masu kamanceceniya