Da Dumi-Dumi

Covid-19 ta dakatar da ci gaban aikin fim din The right choice -Jammaje

blogger@northflix.ng 2020-04-03 15:40:20 Labarai

A daidai lokacin da a ke tsaka da gudanar da shirye-shiryen komawa wuraren da a ke aikin fim din The right choice, ciki harda babban birnin tarayya Abuja, sai ga shi kuma an samu kai cikin yanayi na annobar Covid-19 wanda ta zama barazana ga lafiyar al’ummar duniya ta kuma tsayar da komai.

Tun a cikin watan Janairun da ya gabata ne dai a ka fara aikin fim din wanda a ka shafe tsawon sati biyu a na yin aikin tun daga ranar 26 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabarairu na shekarar nan, wanda a ka tsara za a kammala aikin a daidai lokacin. To sai dai wasu matsaloli da su ka biyo baya ya sanya ba a samu damar kammala aikin ba a daidai lokacin da a ka tsara, domin haka ne ma a ka mayar da karashen aikin zuwa 10 ga wannan watan na Afrilu, domin a samu a karasa aikin.

To sai dai a yanzu, saboda yadda matsalar cutar Covid-19, ta sanya aikin ba zai kammalu ba, dole sai dai a sauya wani lokacin domin yin karashen aikin.

Malam Kabiru Musa Jammaje, shi ne babban mashiryin fim din, domin haka mun ji ta bakin sa dangane da halin da a ke ciki dangane da aikin karashen fim din, wanda ya shaida mana cewar.

"To gaskiya da mun tsara a wannan watan za mu koma Abuja domin kammala aikin fim din The right choice, wanda mu ka fara yi tun cikin watan Janairu, to amma duba da yadda a ke ciki a yanzu, hakan ya sa dole mu ka ajiye maganar karasa fim din. Duk da cewar kusan kashi 80 cikin 100 na aikin mun gama shi, domin haka kashi 20 cikin 100 ne yanzu ya rage mana, domin haka a yanzu za mu jira mu ga yadda yanayi zai bayar nan gaba, sannan mu kara tsayar da wata sabuwar ranar, amma dai a yanzu mun dakatar da aikin har zuwa lokacin da hali zai bayar a yi".

Dangane da yadda aikin ya gudana kuwa, Kabiru Jammaje, ya ce,"An yi aikin cikin nasara, saboda haka mu ke da karfin gwiwar karashen fim din, kuma za mu samu nasara fiye da wanda mu ka samu a baya, domin haka a kwai nasara a cikin aikin". Inji Jammaje.

Fim din The right choice dai wani gagarumin fim ne da a ke ganin kusan shi ne fim na farko da wani dan masana'antar fina-finai ta Kannywood ya shirya wanda ya lashe miliyoyin kudi a tarihin masana'antar, domin kuwa a na kiyasin cewar fim din zai lashe zunzurutun kudi har Naira miliyan 35 kafin a kammala shi.

Baya ga haka fim din ya kun shi manyan jarumai na masana'antar fina-finai ta Kannywood da kuma na Nollywood, wadanda su ka hadar da Ali Nuhu, Abba Almustapha, Asabe Madaki, Sani Mu'azu. Sai kuma daga 'yan Nollywood akwai jarumai da su ka hadar da Segun Arinze, Nancy EIsime, Enyinna Nwagwe, da sauran su.

Malam Kabiru Musa Jammaje ya bayyana alhinin sa dangane da halin da duniya ta samu kan ta a ciki na wannan annobar ta cutar Covid-19, kuma ya yi fatan Allah ya kawo mana karshan wannaCovid-19 ta dakatar da ci gaban aikin fim din The right choice -Jammaje

A daidai lokacin da a ke tsaka da gudanar da shirye-shiryen komawa wuraren da a ke aikin fim din The right choice, ciki harda babban birnin tarayya Abuja, sai ga shi kuma an samu kai cikin yanayi na annobar Covid-19 wanda ta zama barazana ga lafiyar al’ummar duniya ta kuma tsayar da komai.

Tun a cikin watan Janairun da ya gabata ne dai a ka fara aikin fim din wanda a ka shafe tsawon sati biyu a na yin aikin tun daga ranar 26 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabarairu na shekarar nan, wanda a ka tsara za a kammala aikin a daidai lokacin. To sai dai wasu matsaloli da su ka biyo baya ya sanya ba a samu damar kammala aikin ba a daidai lokacin da a ka tsara, domin haka ne ma a ka mayar da karashen aikin zuwa 10 ga wannan watan na Afrilu, domin a samu a karasa aikin.

To sai dai a yanzu, saboda yadda matsalar cutar Covid-19, ta sanya aikin ba zai kammalu ba, dole sai dai a sauya wani lokacin domin yin karashen aikin.

Malam Kabiru Musa Jammaje, shi ne babban mashiryin fim din, domin haka mun ji ta bakin sa dangane da halin da a ke ciki dangane da aikin karashen fim din, wanda ya shaida mana cewar.

"To gaskiya da mun tsara a wannan watan za mu koma Abuja domin kammala aikin fim din The right choice, wanda mu ka fara yi tun cikin watan Janairu, to amma duba da yadda a ke ciki a yanzu, hakan ya sa dole mu ka ajiye maganar karasa fim din. Duk da cewar kusan kashi 80 cikin 100 na aikin mun gama shi, domin haka kashi 20 cikin 100 ne yanzu ya rage mana, domin haka a yanzu za mu jira mu ga yadda yanayi zai bayar nan gaba, sannan mu kara tsayar da wata sabuwar ranar, amma dai a yanzu mun dakatar da aikin har zuwa lokacin da hali zai bayar a yi".

Dangane da yadda aikin ya gudana kuwa, Kabiru Jammaje, ya ce,"An yi aikin cikin nasara, saboda haka mu ke da karfin gwiwar karashen fim din, kuma za mu samu nasara fiye da wanda mu ka samu a baya, domin haka a kwai nasara a cikin aikin". Inji Jammaje.

Fim din The right choice dai wani gagarumin fim ne da a ke ganin kusan shi ne fim na farko da wani dan masana'antar fina-finai ta Kannywood ya shirya wanda ya lashe miliyoyin kudi a tarihin masana'antar, domin kuwa a na kiyasin cewar fim din zai lashe zunzurutun kudi har Naira miliyan 35 kafin a kammala shi.

Baya ga haka fim din ya kun shi manyan jarumai na masana'antar fina-finai ta Kannywood da kuma na Nollywood, wadanda su ka hadar da Ali Nuhu, Abba Almustapha, Asabe Madaki, Sani Mu'azu. Sai kuma daga 'yan Nollywood akwai jarumai da su ka hadar da Segun Arinze, Nancy EIsime, Enyinna Nwagwe, da sauran su.

Malam Kabiru Musa Jammaje ya bayyana alhinin sa dangane da halin da duniya ta samu kan ta a ciki na wannan annobar ta cutar Covid-19, kuma ya yi fatan Allah ya kawo mana karshan wannan musifa da ta zama barazana ga al'umar duniya baki daya.n musifa da ta zama barazana ga al'umar duniya baki daya.

Labarai masu kamanceceniya