Da Dumi-Dumi

Zan bada tallafin kayan Abinci saboda Coronavirus –Maryam Booth

blogger@northflix.ng 2020-04-01 11:31:22 Labarai

 

Jarumar Maryam Booth ta ci alwashin bada tallafi buhun shinkafa har guda 100 da kwalin farin magi guda dari da kuma jarkar mai guda 50 ga ‘yan gudun hijira domin su nutsu a gidajen su kar su fita neman abinci saboda cutar coronavirus.

Jarumar ta bayyana haka ne a shafin zumuntar ta na Twitter, inda take neman duk wanda yasan inda ‘yan gudun hijira su ke a sanar da ita domin bada tallafin ta.

Da yawa daga cikin mabiya Maryam Booth a shafin na ta sun sun nuna jindadin su bisa wannan al’amari na bada tallafin, inda suke ta yaba mata tare da fatan alkhairi a gareta.

Sai dai wasu daga cikin mabiyan na ta sun nuna mata cewa ba iya ‘yan gudun hijira ya kamata ta baiwa wannan tallafi ba, kamata ya yi ta nemi unguwar talakawa da mabukata ta basu wannan tallafi domin da yawa akwai mutane mabukata wadanda abinci ya gagare su basu da cin yau bare na gobe wanda ‘yan gudun hijira ma sun fisu gata.

Labarai masu kamanceceniya