Wannan shathi yayi kyau Sosai, Duk da cewa bam kalli films dinba tukunna
A farkon fim din an nuna Alhaji Teku (Sulaiman Bosho) tsaye a gaban motarsa, yayin da wasu matasan kauyensu ka zo don gaisawa da shi amma sai ya nemi gayawa mahaifin su bakar magana, da su ka nuna rashin jin dadinsu a kan haka kuma sai ya sa yaron gidan sa ya raka su da duka.
Alhaji Teku ya kasance attajirin kauye wanda babu kamar sa a fannin dukiya domin an nuna kaf fadin kauyen shi kadai ne yake da motar hawa, hakan ne yasa ya zamo mutum mai jiji da kai wanda ba ya daukar raini a wajen kowa.
Sai dai kuma duk yawan dukiyar tasa ba ta amfanar mutanen kauyen da komai, domin ba ya kyauta ko sadaka haka kuma a cikin gida ma bai wadata iyalan sa da dukiyar tasa ba, kuma mutum ne shi mai siya wa kansa raini, domin hatta daya daga cikin matansa ba ta ganin darajarsa (Halima Atete). Domin duk lokacin da rigima ta hado ta da kishiyar ta da zarar Alhaji Teku ya saka baki don neman sulhu a cikin rigimar haka ta ke yi ma sa zagin cin mutunci, wanda sanadin hakan ya sa Alhaji Teku ya sake ta.
Babbar matsalar Alhaji Teku ita ce, yawan son mata domin ya na da budurwar zuciya ba ya duba yawan shekarunsa, duk lokacin da ya kyallara ido ya ga mace musamman kananan yara ‘yan mata sai ya makale mu su ya dinga kashe musu kudi don su aure shi. A irin hakan ne ya raba Habu (Saifullahi S. Fulani) da budurwar sa wadda ta ke ikirarin cewar ta na kaunar sa, amma daga lokacin da Alhaji Teku ya sakar ma ta kudi sai ta guji saurayin ta wato Habu ta koma ga Alhaji Teku.
Haka kuma shima Dan Marka (Garzali Miko) wanda ya kasance dan uwa ga Alhaji Teku a koda yaushe samun sabani suke da Alhajin domin yakan je neman taimako wajen Alhajin amma sai ya hana sa, wanda sanadin hakan ke fusata Dan Marka saboda ganin Alhaji bai rasa abinda zai taimake sa dashi ba, yayin da kuma Hauwa (Hassana Muhammad) take jin haushin Dan Marka a duk lokacin da yaje neman taimako bai samu ba, da zarar ya soma fada sai ta dinga ganin rashin hakurin sa wanda a karshe ma tayi yaji ta koma gidan su kuma ta bukaci Dan Marka ya sake ta. Lokacin da matar Dan Marka ta guje sa sai yaje wajen Alhaji Teku don yasa baki ga iyayen ta matar sa ta dawo gidan sa.
Amma sai Alhaji yaki yin hakan karshe ma bayan Dan Marka ya saki matar tasa Hauwa sai Alhaji Teku ya zagaye ya aure ta. Haka bayan Dan Marka ya sake yin wani auren Alhaji Teku ya raba sa da matar tasa, fushin hakan ne yasa Dan Marka da wasu jama’ar wadanda basa goyon bayan Alhaji Teku suka je gidan sa da nufin yi masa duka, amma sai ya gudu wajen maigari. Sanadin hakan ne yasa aka soma neman Dan Marka za’a yi masa hukunci amma sai mahaifiyar sa Marka (Hajara Usman) ta bashi shawarar ya tafi birni neman sana’a.
Cikin sa’a kuwa Dan Marka ya dawo daga birni da dumbin arziki domin ya sayi mota me tsada kuma ya taho da budurwar da zai aura. Yayin da a lokacin tuni arzikin Alhaji Teku ya soma ha baya. Ita kuma Hauwa tsohuwar matar Dan Marka tuni Alhaji Teku yayi mata saki uku yayin da ta saura yana nadama.
Haka ma Ladidi matar sa ta biyu da ta guje sa (Amal Umar) nan itama ta soma nadamar gujewa Dan Marka kuma ta bukaci ya mayar da ita dakin ta saboda ganin yayi kudi amma sai ya nuna lokaci ya kure mata don shi tuni ya taho da matar da zai aura.
Abubuwan Birgewa:
Kurakurai:
Karkarewa:
Labarin ya nishadantar sosai kuma ya rike me kallo, haka kuma an yi kokarin isar da wani darasi na illar cin amana da kwadayi ko gujewa masoyin gaskiya saboda bashi da abin duniya, wanda a karshe hakan ya jefa mutum cikin nadama da danasani.