Mahaifin Ali Nuhu Ya rasu

blogger@northflix.ng 2020-06-08 11:08:48 Labarai


Labarin da mu ka samu daga jihar Gombe a yammacin wannan rana ta Litinin 8 ga watan Yuni Allah ya yi wa mahaifin fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu wato Mista Nuhu Palloma rasuwa. 
Marigayin dai fitaccen dan siyasa ne a jihar Gombe kafin rasuwar sa, wanda a nan gaba kadan za a yi jana'izar sa. Sai ku saurare mu domin jin cikakken labarin a nan gaba fatan Allah ya bai wa Ali Nuhu juriyar rashin da ya yi.

Labarai masu kamanceceniya