Tumbatsar da Kannywood ta yi mu ke samun matsala - Salisu Muhd Officer

blogger@northflix.ng 2020-07-30 16:35:20 Labarai


Tun bayan zaben shugaban kungiyar kwararru masu shirya fim ta kasa (MOPPAN) a ke zuba idanu, domin a ga irin kamun ludayin shugabanin, da kuma irin ayyukan da su ka kudirci niyar yi wa masana'antar fina-finai ta Kannywood, saboda dumbin matsalolin da su ka dabaibaye ta. To sai dai yau sama da shekara guda Kenan, har yanzu ba a ga inda tsarin shugabancin ya fara motsawa ba. Kan wannan batun ne mu ka nemi jin ta bakin daya daga cikin shugabanin kungiyar, domin sanin dalilin da ya sa har zuwa yanzu a ke ganin ba su fara aikin da masana'antar za ta san an samu canjin shugabanci ba.
Salisu Muhammad Officer ya na daya daga cikin shugabanni a matakin jihar Kano da kuma kasa baki daya. A hirar da su ka yi da wakilin mu ya bayyana dalilin da ya sa mutane har yanzu ba su fara gani a kasa ba. Inda ya fara da cewar.
"To gaskiya wannan abun ba haka ya ke ba, domin ma su cewa har yanzu shugabancin (MOPPAN) har yanzu bai yi wani abu ba tun da a ka zabe mu, abun ba haka ya ke ba. Duk da ya ke mu ma mu na da laifi, amma dai akwai abubuwa hawa-hawa, sai dai mu na kokari mu na aiki, sai dai ba ma fitar da shi mu na bayyana shi a ko'ina, har sai abubuwan da mu ka tsara sun tabbata, sannan mun samu matsala ta zuwan Corona wanda ya tsayar da harkoki a duniya, to mu ma abun ya shafe mu, domin in ka kalli duniyar gaba daya a tsaye take, saboda wannan matsalar ta Corona, to wadanda na daya daga cikin abubuwan da ya sa mutane ba sa ganin komai, domin rabon da a ce mun zauna taron kungiyar ma yau wajen wata 6 kenan, domin haka wannan su ne su ka kawo dabaibayi a aikin mu, kuma mu na nema a gwamnatance mu ga yadda za mu samu abubuwan da za mu yi alfahari da shi, wanda za mu kyautata wa mutanen mu".
Dangane da halin ko in kula da a ke zargi su na nuna wa ga harkokin masana'antar kuwa, Salisu Muhammad Officer cewa ya yi.
"E gaskiya ne akwai abubuwa da yawa na ko in kula, wannan kuma ya biyo bayan tumbatsar da masana'antar ta yi ne. Tun farko mun yi ta kokarin samun hanyar da za a bi domin a tantance su, kuma shiri ya yi nisa, to mun zo za mu fara a kungiyance, sai kuma matsalar Corona ta zo, amma dai mu na nan mu na kan tsarin, domin idan ba tsari a ka yi ba a masana'antar da yi mata katanga, to lallai za a ci gaba da samun matsala a cikin wannan masana'antar, domin ta cika ta tumbatsa da wanda mu ka sa ni da wanda ba mu sa ni ba, sun shigo cikin ta, kuma wadanda ba shugabanni ba, ba sa taimakon mu, su na daukar su na saka su a fim, domin su saka a irin fina-finan nan na YouTube, sai su rinka daukar irin wadannan yara su na sakawa, yanzu idan ka na so ka yi fim ka kira taron tantance wadanda ka ke so su fito a fim din, yanzu nan sai ka ga yara sama da dubu, to irin wannan ya za mu yi da su? Me mu ke da shi da za mu ba su. To mun tsara za mu yi wa abun katanga, sai wannan matsalar ta Corona ta zo domin haka sai shirin ya wargaje, tun daga nan babu wani abu da mu ka iya shiryawa har zuwa yanzu".
Ko wanne darasi ku ka samu domin gyaran gaba?
"To mun samu darasi, saboda ya kamata, mu koyi zama da irin duk wata matsala da ta zo, mu taka rawar mu daidai da yanayin da muka samu kan mu a ciki, wannan shi ne daya daga cikin darasin da mu ka samu, duk da wannan matsalar ta Corona da ta zo, da shugabanci ta na kokarin yin wani abu na gudanar da shugabanci, to da yanzu abubuwan ba su kai haka lalacewa ba, amma yanzu ko bayan wannan Annobar za ka ga kafin mu shawo kan matsalar za mu sha wuya sosai da gaske, mun samu darasi a wannan matsalar ta Corona, yanzu masana'antar babu jari, babu da'a, kawai mu na zaune kara zube saboda watsi da mu ka yi da shugabancin, tun da cutar Corona ta zo sai kawai mu ka koma mu na yakar junan mu, maimakon mu saka ci gaban masana'antar a gaba, domin haka mu na kira ga masu kallon mu su yi hakuri shugabanci ya na nan ya na kokarin yadda zai shawo kan lamuran, domin a sabunta harkar yadda kowa zai ji dadin yadda a ke gudanar da ita". Inji Salisu Muhammad Officer

Labarai masu kamanceceniya