Ina tafiya kawai sai na ji sara a kai na - Mawakiya Ummi Kano

blogger@northflix.ng 2020-08-07 10:31:25 Labarai


Aisha Isah Usman wadda a ka fi sani da Ummi Kano ta yi wakoki da dama da su ka shafi zamantakewa da yabon Annabi (S.A.W) da kuma wakokin siyasa a rayuwar ta.
Sai dai kuma Ummi Kano ta yi fadi tashi a cikin harkar kafin ta kai ga duniya ta san ta, wakilin mu ya tattauna da ita domin haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance.
Da farko za mu so ki gabatar da kan ki.
“To da farko dai suna na Aisha Isah Usman, amma dai an fi sani na da Ummi Kano, kuma asalin sunan kakata ne wadda ta haifi Babana, kuma a Kano a ka haife ni a Rafin Kuka dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, shekaru na a yanzu 25, ta bangaren karatu kuma na yi makarantar firamare ta Ja'oji, da na gama na shiga Sakandare ta Gandun Albasa, amma ban kammala ba a ka cire ni a ka yi mini aure, daga nan kuma ban ci gaba ba”.
To ya ya a ka yi kika fara harkar waka?
“E to gaskiya sha'awa ce, domin tun kafin na yi aure ina dan jin dadin wakar har ya zama na fara, amma dai asalin wakar da na fara yi ta yabo ce. Domin a lokacin ba zan manta ba na kan je wajen maigida na Tijjani Gwandu ya rubuta mini sai na dora, amma dai akwai marubucin waka ta wanda har yanzu shi ne ya ke rubuta mini waka wato Aliyu Musa Nassarawa. To bayan aure na ya mutu ne sai na ci gaba da yin wakar, wanda kuma na fi karkata ga wakokin siyasa da na soyayya kuma wakar da ta yi fice a ka sanni da ita a fannin soyayya ita ce so da kauna. A wakar siyasa kuma wadda a ka sanni da ita wakar mai Amana daga tafiyar Amana, wadda na yi wa Abba Kabir Yusif wato Abba Gida-Gida. Sai kuma wakar da mu ka hau mu biyu ni da Ali Art work ita ce Ga Zaki ma ci abokan gaba. Akwai wakoki na siyasa ma su yawa da ba za su lissafu ba, haka ma na soyayya”.
Ku mawakan siyasa ba ku damu da yin kundi na waka ba ko me ya sa?
“To saboda ka san ita wakar siyasa a na yin ta ne a daidai lokacin da a ke yakin neman zabe, domin haka ne za ka ga ba mu damu da mu yi kundin waka ba, sai dai mu yi ta turawa mutane, amma wakoki na soyayya a yanzu ma ina dora su a YouTube”.
To ko ya ya Ummi Kano ta dauki harkar waka?
“Gaskiya waka sana'a ce kuma mun samu alheri a cikin ta, domin ta sanadiyyar waka an ba ni Mota, kuma na samu alheri mai yawa har yanzu ma ina ci gaba da samu, saboda ba zan manta ba da wani tsautsayi ya same ni duk manyan 'yan siyasar nan babu wanda bai taimaka mini ba Abba Gida-Gida, Jagoran mu Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da sauran jama'a duk sun tallafa mini, a nan na kara tabbatar da cewar ina da kima a wajen mutane”.
Ko wanne irin matsaloli ki ka samu a harkar ki ta waka?
“To babbar matsalar da na samu shi ne wadda ina tafiya a kan hanya mutane su ka tare ni su ka sassara ni, su ka sace mini wayoyi na, Allah ne ma ya yi da sauran raina. Amma dai cikin ikon Allah Abba Gida-Gida ya sa a ka kaini asibiti na samu lafiya, amma duk wanda ya ga yadda a ka ji mini ciwo ya san na sha wahala, amma cikin sati biyu na warke”.

Menene sakon ki na karshe?
“To sako na shi ne, ina kira ga mawaka su rike sana'ar su ta waka da muhimanci, domin sana'a ce da take da rufin asiri, kuma ni na ga hakan, kuma ina fatan Allah ya hada kan mu”. A cewar Ummi Kano.

Labarai masu kamanceceniya