Dadin Kowa: dalilin shirin na yi suna a duniya - Dantani mai shayi

blogger@northflix.ng 2020-08-08 13:53:02 Labarai


Ga duk wanda ya ke kallon shirin Dadin Kowa na Arewa 24 ya san Dantani mai shayi wato Murtala Alhassan, saboda irin rawar da ya taka a cikin shirin, musamman yadda su ke gudanar da harkar su da Sallau a matsayin yaro da Uban gida.
Murtala Alhassan ya yi gwagwarmaya a iya tsawon rayuwar sa har ya kawo wannan matakin cikin shirin. Domin jin ko wanene Dantani mai shayi wakilin mu ya tattauna da shi ga kuma yadda tattaunawar ta su ta kasance kamar haka.
Za mu so ka gabatar da kan ka ga ma su karatun mu?
“To ni dai suna na Murtala Alhassan, wanda a Shirin Dadin Kowa a ka sanni da Dantani mai shayi, sannan a wasan Dabe da mu ke yi a ka sanni a Karabiti. Kuma ni haifaffen unguwar Birget ne a cikin garin Kano, a nan a ka haifeni a 1984. Kuma tun ina karami iyaye na su ka taso su ka koma unguwar Badawa da zama, a nan na girma na yi makarantar firamare na yi Sakandare, kuma tun daga nan ne harkar Dirama ta shiga zuciya ta, tun mu na yin na makaranta har wani lokaci ba na mantawa Dalha Musa Dakata wanda a Dirama a ke kiran sa da Dandano, su ka kawo mana kungiyar Dirama a nan unguwar mu, to ta nan a ka fara koya mini wasan Dabe, kuma har na samu sunan Karabiti, to haka dai mu ka yi ta ci gaba kungiyar mu ta na haba ka, to daga nan dai har mu ka fara fitowa a fim, domin ba zan manta ba, fim din da na fara fitowa a cikin sa shi ne Dan Adam Butulu, wanda na fito a matsayin maigadi, to daga nan dai likkafa ta ci gaba sai wani ya dauke ni mu ka tafi Abuja mu ke yi a can, to mu na can sai Allah ya kai Umar Kanu, sun je tare da Fati Muhammad kuma daman da ya ke mun san juna da ita saboda mun yi fim tare, saboda haka sai Umar Kanu ya ce to ai kai bai kamata ka zauna a nan ba, ka zo mu tafi tare. Ya na kawo ni Kano sai ya hada ni da Ali Jita, a lokacin ma bai shahara ba ya ce mu rinka aiki tare, domin haka kusan a harkar fim kowa da Ali Jita ya sanni, ba ni da wani mai gida sama da shi har yanzu. To daga nan sai ya zama ina shiga wa su ayyuka na fim da mutane su ke yi su kan ba ni aiki na bayan kyamara, har ma ya zama a kan ba ni sin daya ko biyu, sai kuma a rinka cewa abun da na yi ya burge jama'a, ni kuma abun ya na kara shiga zuciya ta, to a na nan sai wani lokaci Nazir Adam Saleh ya kira ni ya ce ga shi wani fim za a fara mai dogon Zango, kuma a na son ka fito a matsayin mai shayi, kuma da na gwada a ka ce ya yi, a lokacin ma ba Umar Jigirya ba ne a matsayin Sallau wani ne daban sai daga baya ya samu damar shiga matsayin Sallau. To a lokacin da a ka fara ba na gari, kuma ban ma san muhimancin abun ba, domin haka sai a ka yi ta kira na a waya ina cewa gobe zan dawo jibi zan dawoa har ma a ka ce a cire ni, amma da Allah ya sa ina da rabo sai Daraktan ya yi ta ba ni lokaci har dai na dawo. Kuma da ya ke tanan Allah ya yi duniya za ta sanni, ka ga duk wancan gwagwarmaya da a ka sha a baya, sai ya zama tahiri, a yanzu duk inda na je a duniya a na kallo na a na kira na, domin haka babu abun da zan ce sai godiya ga Allah”.
Wai kafin wannan fim din na Dadin Kowa, ko ka taba yin sana'ar Shayi ne?
“Gaskiya a rayuwa ta ban taba yin sana'ar shayi ba, ban ma san yadda a ke yin sa ba. Amma dai da a ka dora ni a wannan rol din da kuma yadda na ga a na karrama ni, sai abuin ya kara shiga zuciya ta, har ta kai ta kawo sai na je na zauna a wajen mai shayi, domin na ga yadda ya ke mu'amalar sa da ma su sayen shayin sa, sai na rinka yin amfani da shi a cikin shirin Dadin Kowa”.
A cikin shirin an fi sanin ka da Yaron ka Sallau, ko ya ka ke ganin yadda ku ke fafatawa?
“To ka ga dai tun a farko Sallau da shi da Dalha su ne su ka koya mini Dirama, yau kuma sai ya zama a cikin Dadin Kowa, ni ne maigidan sa, to gaskiya na ji dadi, domin idan za mu yi aiki ya na fitowa a Matsayin yaro ni kuma maigidan sa, amma idan mu ka gama fim din kuma shi ne maigida na, kuma gaskiya ina jin dadin kasancewar mu da shi, saboda idan ya ga wani waje ban yi daidai ba ya kan gyara mini, to ka ga kauna ce kuma ina jin dadin wannan sosai”.
Da yake ka yi suna a duniya ko ya ya ka ke kasancewa idan ka je wani gari?
“To gaskiya duk inda na shiga a fadin duniya da dama, domin ban taba zaton haka nake da suna ba a duniya sai da wata tafiya ta shigar da ni Nijar, wallahi irin jama'ar da na gani, abun sai da ya tsora ta ni, kuma duk inda na je a na dauka ta mai shayi, kuma wannan tambayar da ka yi mini ta cewar ina shayi haka mutane su ke yi mini a duk inda na je, kuma a yanayi irin namu babu irin jama'ar da ba ma haduwa da su Zaurawan ne 'Yammata ne, wanda kuma a nan mu na samun kalubale wanda dole mu ke yin taka tsantsan da kuma bi a hankali, kowa ya ce ya na son ka, to mace sama da dubu kowacce ta ce ta na so ta aure ka ya ya za ka yi da su, ka ga dole sai a na yin taka tsantsan. Kuma su matan ya kamata dai su rinka yi mana uziri”.
Da ya ke ka na da iyali, ko daga cikin masoyan ka ne na shirin Dadin Kowa ka samu ka aura?
“To gaskiya ba daga cikin su ba ne, domin ita wadda na aura Allah ne ya yi zan aure ta, domin ni daman tun da na taso zan iya cewa kaina matsoraci ne a wajen mata, domin a yadda mu ka taso an yi Isalamiyu a unguwa na je wajen ‘yar wani ni ba auren ta zan yi ba sai na ga ai yaudara ce, domin haka ko da na taso ban saba da zuwa zance ba, domin haka matar da na aura zuwa zancen da na yi har mu ka yi aure bai kai goma ba, domin haka ba ta dalilin Dadin Kowa mu ka hadu ba”.
Ko dai da alamar nan gaba in za ka kara aure a cikin masoyan da ka yi da su za ka yi kari?
“Eh to gaskiya akwai yiwuwar haka din, domin a yanzu ba ni da tunanin zan zauna da mace daya, domin haka duk wadda Allah ya zaba mini tagari, in sha Allah a shirye nake”.
To Menene sakon ka na karshe?
“Sako na a karshe shi ne ina godiya ga jama'a da su ke kauna ta kuma ni ma ina kaunar su, Allah ya bar zumunci ta tare da mu”. A cewar Dan Tani mai shayi.

Labarai masu kamanceceniya