Mun kasa karbar guguwar canjin kasuwanci da zamani ya kawowa Kannywood - Usman Mu’azu

blogger@northflix.ng 2020-08-10 14:40:06 Labarai


Fitaccen Furodusa wanda ya dade ya na gwagwarmaya tare da farfado da masana’antar Kannywood, Usman Mu’azu, ya bayyanawa cewa kwata-kwata ba su dauki hanya mai bulewa ba, kamar yadda sauran masana’antu fina-finai su ka yi mu su fintinkau a harkar.
Usman Mu’azu cikin zantawar sa da wakiliyar mu ta Northflix, wadda ta yi da shi a kan irin hanyoyin da masana’antar Kannywood za ta tsaya da kafar ta tare da warware matsalolin da masana’antar ta shiga.
Cikin zantawar su, Usman Mu’azu ya ce” Rashin ilimi da kuma rashin bin hanyar kasuwancin da ragowar masana’antar shirya fina-finai su ka yi, shi ya sanya Kannywood har yanzu ta zama koma baya a bangaren shirya fim”.
Kasancewar ka Furodusa wanda ya dade ya na juya akalar Kannywood tare da shirya fina-finai ma su kyau a masana’antar, me ya sa ka ja baya da harkar yanzu?
“Ba ja baya na yi ba, kawai dai kin san an ce idan kida ya canja, dole rawa ma ta canja, hasali ma na je na karo karatu a kasar Indiya, domin na yi karatu a kan fannin da ya shafi harkar fim kamar yadda ya ke a matsayin sana’a ta, sai na ke ganin cewa bai kamata na dawo na yi fim irin wanda a ka saba yi a baya ba, ni ma ina so na yi fim kamar yadda a ke yi a duniya, wannan dalilin ya sa na fito na yi wani shiri na musamman, domin na shirya wani fim wanda a duniya kowa zai yi alfahari da shi, wato gawurtacce a nan gaba kadan wanda zan fito da ainihin yadda a ke fim a duniya”.
Ya ka ke ganin zamanin da ka yi fina-finai ma su fadakarwa wanda har ka samu damar zama fitaccen Furoodusa, wanda a yanzu kamar ya sha banban da irin na ku?
“A na samun karin ci gaba a bangaren kayan da a ke aikace-aikacen fina-finai, amma kuma akwai inda a ka bar mu a bayan tsarin, domin za ka raba fina-finan su fita duniya ta gani, kamar dai yadda kasashen Turai da sauran takwarorin mu su ke yi ba mu dau layi daya ba, saboda ganin yadda ayyukan can su ke tafiya da kuma yadda su ke bi su saki fina-finan su. To mu mun dogara ne da kasuwar cikin gida, kuma kasuwa guda daya wanda shi ya bada dama har masana’antar a ke ganin ta durkushe, sannan kuma akwai Furodusoshi matasa da su ke a matsayin Furodusas yanzu, gaskiya su na kokari sosai, sai dai ina kara kira a gare su da mu hakura mu zo mu koma makaranta mu karo ilimin shirya fim kamar yadda a ke a duniya ba yadda mu ke yi ba, domin yadda mu ke ba haka a ke a duniya ba, babu inda a ke fim a ce mutum daya ne zai dau nauyin fim gaba daya shi ne wato ‘fim joint venture’ kamar mu hada hannu da hannu a bangaren kasuwancin fim tare da gugun matasa ko kamfanoni, domin a fito da wani abu mai kyau wanda duniya za ta gani ta amfana”. 
Ka na ganin kasuwancin fina-finai a YouTube da Manhajoji mafita ce ga Kannywood din bayan rugujewar kasuwar faifan CD da na DVD?
“Ci gaba ne, amma ci gaban me hakan rijiya, saboda YouTube kawai ba zai iya rike ka ba, dole sai an hada kai an yi wani shafi kamar irin na ku din nan, kuma ya kamata a raja’a a Manhajar Northflix a taimaka ta mike mu ma ta taimake mu, sannan mu samu abun da mu ke so, domin ci gabane, kuma duk sauran kasashen duniya da takwarorin mu su na da Manhaja kwatankwacin Northflix din nan, kuma ta haka su ke taimakawa juna, amma wani YouTube duk babu inda zai kai mu gaskiya. Ina ganin gaskiya wani bude YouTube Channel da tallata fina-finai a nan ba shi ne mafita ba gaskiya, mafita daya ce wadda ni a iya yawon da na yi da kuma karin karatu da  na yi a kan harkar fim shi ne, idan da yau za mu raja’a a kan wannan Northflix din, to ina ga ya wadatar da mu abun da mu ke nema, kamar yadda mu ka sa mu kasuwar cikin gida wato ‘local market’ a baya, sai mu samu kuma ‘Digital market’ a wannan Manhajar ta Northflix din, tun da mutane ne wadanda su ka zo haka kawai, domin su ciciba masana’antar Kannywood , domin haka sai mu ba su hadin kai kowa ya samu ya karu da kowa”.
Akwai wata gudunmawa ko hange da ka ke wa masana’antar, kasancewa duk manufar guda daya ce, domin kawo ci gaban da za a samu a cikin masana’antar?
“Eh gaskiya akwai, musamman saboda ya zamana har kullum shi harshen Hausa ya zamana harshen da ya fi kowanne yawa da yaduwa a nahiyar mu ta Afrika. To ina ganin idan mu ka fara shirye-shiryen mu za mu rinka samo labarai ma su ma’ana wanda su ke fitar da sako, sakon kuma da zai warkar da wata matsala da ta addabi al’ummar mu, to ba karamin ci gaba za a samu ba gaskiya, domin haka ina son mu hada kai mu kuma gyara tsare-tsaren fim da kuma ayyukan mu da labaran mu daga marasa ma’ana zuwa ma su ma’ana, domin kuwa idan mun yi mai kyau za mu ga mai kyau a cewar ma su iya magana“. A cewar Usman Mu’azu.

Labarai masu kamanceceniya