Yawancin mu makafi ne a Kannywood - Babangida Bangis

blogger@northflix.ng 2020-07-25 15:44:22 Labarai


An bayyana kasuwancin fina-finai da masana'antar Kannywood ta runguma a yanzu cewa, harka ce da ita kadai ba za ta iya rike masana'antar ba. 
Furodusa jarumi kuma Darakta a masana'antar, Babangida Bangis ne ya furta hakan a yayin tattaunawar su da da wakilin mu.
Da farko ya fara da cewa "Allah ne da zamani, domin ba zan manta ba a can baya da a ke yin harkar a cikin kaset na bidiyo mutane su ke cewar nan gaba wannan harkar za ta yi bunkasar da za ta bayar da mamaki, to sai mutane su ke ganin kamar ba zai yi wu ba. To da CD ya zo sai mu ke ganin kamar an kuma kai makura, to sai gashi harkar yanzu ta dawo YouTube da sauran su, to wannan ba wani abu ba ne, domin shi tsarin duniya ya na iya sauyawa. Sai dai duk da irin ci gaban da a ka samu, idan ka duba masana'antar za ka ga da yawa su na shan wahala ne, saboda ba su san inda su ka dosa ba, domin ba su ma san menene YouTube din ba ma, su na yin sa ne dai kawai, saboda yawacin mu makafi ne a kan harkar, domin sai ka ga mutum ba shi da sana'ar yi a cikin masana'antar, wani dan aiki ya ke yi wanda ba zai iya rike kan sa da shi ba, amma sai ka ga wai ya bude YouTube kuma ba shi da wani abu da zai zuba a ciki, wanda idan za ka tambaye shi abun da zai ci a cikin sa bashi da shi, aikin da ya ke yi ma ba ya samuwa kuma ba a neman sa, saboda bai yi fice ba, amma wai ya bude YouTube ya na jiran su ba shi kudi, amma dai akwai wadanda su ka bude kuma su na samun kudi da YouTube din. Sai dai ni a tunani na bai kamata a ce an raja'a a kan YouTube kadai ba, domin shi kadai ba zai rike mu ba a yanzu, dole sai mun samo wasu hanyoyin da za mu rinka tallata kayan mu yadda za su karbu a duniya". A cewar Babangida Bangis.
Sai dai kuma kafin rufewar bakin sa yi kira ga abokan sana'ar sa da su yi kokarin gano hanyoyin da za su tallata fina-finan su, ba wai kawai su tsaya ga iya YouTube kadai ba.

Labarai masu kamanceceniya