Kannywood: Wacce jaruma Ali Nuhu zai aura

blogger@northflix.ng 2020-07-30 16:24:48 Labarai


Fit-a then jarumi a masana’antar Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu ya wallafa wasu hotuna a shafin sa na sada zumunta, wanda hotunan su ka rikita shafukan sada zumuntan, sakamakon ganin hotunan da ba a taba ganin irin su ba ko kuma makamancin su.
Ranar Litinin 27 ga watan Yuli ne dai jarumi Ali Nuhu, ya saki sababbin hotuna a shafin sa na Instagram, bayan ya boye dalilin sakin hotunan, wanda ya sanya mabiya shafukan sada zumunta su ke daukar kamar jarumin aure zai kara a nufin su.
Sai dai da mu ka bincika dalilin sakin wannan hotunan na Ali Nuhu, sakamakon ce-ce-kucen da a ke ta yi tare da ya madidi a kai, wanda ya kuma yamutsa hazo sosai a shafukan sada zumunta, sakamakon kamar cewa Ali Nuhu karin aure zai yi, saboda ganin wannan hotunan da ya saki a shafin na sa. 
To amma dai da Northflix mu ka yi bincken kwakwaf, domin ankarar da mabiya shafukan sada zumunta wajen ganin mun fesa mu su gaskiyar al’amarin tare da sanin halin da a ke ciki, kawai sai mu ka samu labarin ce wa anyi hoton ne, domin daukar wani shirin fim mai suna "GORAN GIDAN BIKI" wanda Mc Malam Ibrahim Sharukhan yake dauka duk shekara, domin bayyana yadda yake ayyukan sa na gidan biki da kuma suna ko kuma wani taron idan an dauke shi wajen tsarawa.
Kuma mun samu labarin cewa wannan sabon shirin na Goron Gidan Biki, za a fara daukar shirin ne nan bada jimawa ba.

Labarai masu kamanceceniya