Sabon salon da Rarara ya fito da shi ya rikita matasa

blogger@northflix.ng 2020-09-10 16:42:30 Labarai

 

A cikin ‘yan kwanakin nan da su ka gaba ya, matasa ke ta kokarin ganin sun lashe kyautar da fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu wanda a ka fi sani da RARARA ya saka.
Mawakin ya dai saka kyaututtuka ne gasar rawa tsakanin matasa maza da mata cewa duk wanda ya samu nasara zai iya lashe kyautar dankareriyar Mota ga wanda ya zao na daya sai Babur din Adaidaita Sahu mai taya Uku ga wanda ya samu nasara a matsayi na biyu, a yayin da na Uku kuwa zai lashe kyautar Babur mai taya biyu, sai na Hudu zai lashe kyautar Naira Dubu Dari da Hamsin, kai kyautar ba a nan ta tsaya ba, domin kuwa har zuwa na 10.
Wannan gasar dai da ya saka a wata rawa na hoton Bidiyo wanda was u jarumai su ka fito a cikin wakar ciki kuwa harda tsofaffin jarumai na Kannywood, sai kuma wa su tsurarrun mawaka wanda ya saba yin waka tare da su da kuma jaruman barkwanci.
A lokacin da a ke daukar hoton Bidiyon an hangi babban furodusa a masana’antar Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda da kuma babban jarumi kuma Darakta, Ali Nuhu tare da mawakain Rararara, wanda su ka dauki hoton Bidiyon wakar mai suna Dogara ya dawo.
Cikin jaruman da a ka hangi fuskar su a ciki awaki: Fati Baffa Fagge wadda kwata-kwata a yanzu ba a ganin ta a cikin fina-finan Kannywood sai Farida Jalal da Hadiza kabara da jaruma mai tasowa, Bilkisu Abdullahi da kuma Aisha Humaira da Rabi’u Daushe da Baba Ari dai sauran jarumai.
Tun bayan kammala wakar da mawakin ya yi tare da bayar da sanarwar garabasar matasa ke ta yunkurin ganin sun lashe wannan gasar. Domin kuwa kusan mutane Dari ne su ka shiga cikin gasar ta mawakin.
Haka zalika daga bangaren mawakin, Dauda Adamu Kahutu Rarara, mun so jin hikimar sa ta saka wannan gasar ta rawa, amma kuma hakar mu ba ta cimma ruwa ba, sakamakon ba mu iya samun sa ba. Amma duk da haka mun yi katarin ganawa da Furodusa, Abubakar Bashir Maishadda, amma duk da haka ba mu samu wani gamsashshen bayani ba, amma kuma ya tabbatar mana da cewa lokacin da a ka saka gasar zuwa yanzu Awa Ashirin da Hudu an samu matasa kimanin 100 da su ka shiga cikin gasar.

Labarai masu kamanceceniya