Kannywod: Ko Maishadda ya na da ra’ayin yin wakokin siyasa kuwa?

blogger@northflix.ng 2020-09-12 05:08:03 Labarai


Fitaccen Furodusa a masana’antar Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda, ya ce baya ga harkokin fina-finai da ya ke yi, a yanzu haka zai kuma karkata bangaren wakokin Siyasa domin bayar da gudunmawar sa a fannin.
Cikin wata zantawa da Maishadda ya yi da wakiliyar mu, dangane da bangaren wakokin siyasa da ya ke kokarin mayar da kai a yanzu haka, har ma ya shirya wakokin kamar irin su Dogara ya dawo da Masari mai hakuri da kuma Jihata tare da Dauda Adamu Kahutu Rarara.
Sai dai duk da kasancewar a kwanakin baya masana’antar Kannywood ta shiga wani yanayi da idan a ka kawo sabobbin fuksa a fim baya karbuwa a kasuwa sai dai ma ya fadi, amma duk da haka shi Furodusan Abubakar Bashir Maishadda ya yi kokarin kawo sababbin fuska da fama kuma fim din ya samu karbuwa, har ta kai jaruman sun yi suna.
Da ya ke a iya cewa Maishadda bai taba shirya wani abu da ya danganci harkokin siyasa ba, sai a wannan lokacin, hakan ya sa majiyar mu ta tambaye shi, shin ko ya na da ra’ayin yin wakokin siyasa ne ko kuwa kawai ya yi ne wannan karon?
Furodusan ya ce “Gaskiya yanzu ina da ra'ayi, musamman ganin yadda shi Dauda Kahutu Rarara ya tsaya kai da fata wajen bada gudunmawar yadda za a gudanar da aikin dari bisa dari tare da shi”. A cewar Abubakar Bashir Maishadda.

Labarai masu kamanceceniya