Kannywood ba za ta taba ruguje wa ba - Abba Al-Mustapha

blogger@northflix.ng 2020-09-04 11:27:07 Labarai


Fitaccen jarumi a masana'antar fina-finai ta Kannywood, Abba Al-Mustapha ya bayyana masana'antar a matsayin babbar masana'anta, duk da kallon da a ke yi mata na ta ruguje wa, inda ya ke cewa Kannywood ta na nan sai ma dai ta ci gaba, ba dai ta ruguje ba.
Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu dangane da yadda a ke kallon masana'antar a matsayin cewar yanzu ta rushe, saboda da halin da a ka samu kai a ciki. 
Jarumin ya fara da cewar "Tun tsawon shekaru idan a ka duba yadda masana'antar ta faro, za a ga cewar ci gaba ta ke yi ba wai ci baya ba, kuma idan ka duba a baya a na amfani da Kaset ne a ka koma CD, sannan a ka koma DVD, wanda kuma a yanzu su ma su ka zama tsohon ya yi, sai kasuwar ta koma gidajen Talbijin da manyan Sinimu, to ka ga a wannan ba ci baya a ka sa mu ba, ci gaba ne, sai dai kalubalen da ya ke gaban mu shi ne, mu samar wa masana'antar ilimin da za mu ci gajiyar ci gaban da a ka samu din".
Ya Kara da cewar" Babbar matsalar masana'antar fina-finai ta Kannywood a yanzu shi ne, rashin ilimin da za mu yi amfani da ci gaban da masana'antar ta samu, domin haka ne a ke ganin kamar masana'antar ta ruguje. Sam Kannywood ba ta ruguje ba, ta na nan ta na kara ci gaba ne, saboda haka Kannywood ta kafu ba kuma za ta ruguje ba, domin yanzu idan ka duba mutanen mu, duk sun koma dora fina-finan su a YouTube, wanda idan har a ka sa mu ilimi a ka yi hakurin gudanar da aikin, to nan gaba za a samu amfanin abun. Sannan kuma ga nuna fina-finai a Sinimu, duk da dai a yanzu yanayin Corona ya tsayar da haska fim a Sinimu, to da zarar an ci gaba za a farfado daga halin da a ka shiga. Baya ga haka ga manyan gidajen Talbijin su na karbar fina-finan mu su na biya, domin su haska a tashar su, to ga wannan wani karin ci gaba ne. Sannan kuma wani karin ci gaba da a ka samu shi ne, manhajar Northflix.ng wadda ita ma a yanzu wata dama ce da mu ka samu a Kannywood, domin tallata fina-finan mu a duniya, domin haka akwai ci gaba sosai da ya zo wa masana'antar, kawai dai su ma su gudanar da harkokin sana'ar su a cikin masana'antar, su yi kokarin samar wa kan su ilimin da za su ci gajiyar abun". Inji Abba Al-Mustapha.
Abba Al-Mustapha ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta duba Allah ta kalli yanayin da a ke ciki ta bude Sinimu, domin farfado da masana'antar fina-finai ta Kannywood, sannan kuma a samar da damar fadada Sinimun, domin bunkasar masana'antar, wadda ta ke da dumbin Matasa da su ke cin abinci a cikin ta.

Labarai masu kamanceceniya