Ilimi Gishirin Rayuwa: Fim din zai sauya tunanin Kannywood - Isah A Isah

blogger@northflix.ng 2020-09-07 06:18:47 Labarai


A cikin satin da ya gabata ne a ka kammala aikin fim din, Ilimi Gishirin Rayuwa, wanda fitaccen jarumi Isah A Isah ya shirya tare da hadin gwiwa da Gidauniyar AMA Foundation.
Fim din wanda a ka shirya shi a birnin Dutsen jihar Jigawa, an kuma shafe tsawon kwanaki a na gudanar da aikin na sa, yayin da kuma kusan dukkan jaruman da a ke ji da su a masana'antar fina-finai ta Kannywood sun fito a cikin fim din.
Bayan kammala aikin fim din wakilin mu ya ji ta bakin Isah A Isah, a matsayin sa na jagoran gudanar da aikin dangane da yadda aikin ya gudana da kuma sakon da fim din ya ke dauke da shi, inda ya kuma bayyana mana cewar "A yanzu dai mun yi aikin fim din, kuma mun kammala cikin nasara, domin haka mu na godiya ga Allah da ya ba mu damar kammala aikin".
Dangane da shirin aikin kuwa cewa ya yi "To ka san shi aiki irin wannan abu ne da sai an shirya shi, saboda haka mun dade da fara shirin aikin, domin mun dauki tsawon lokaci a kan fim din. Saboda shirin mu abun da ya kawo mana jinkiri, yanayin da a ka shiga na Corona, kuma haka ne ma aikin ya kawo har wannan lokacin. Amma dai wani jinkirin alheri ne, mu na fatan hakan ya zama alheri a gare mu".
Ganin yadda a ka kashe wa fim din kudi, ko ya ya za a yi wajen dawo da kudin sa tun da a yanzu kasuwancin fim ya shiga wani hali?
"To gaskiya daman mun shirya wa hakan, domin haka ne ma mu ka zuba kudi ma su yawa, domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu. Domin haka yanzu idan ka duba harkar fim a duniya ta koma online, to ita kuma kasuwar fim ta online ba za ka ji ta da kudi kadan ba, saboda haka mu ka tsaya mu ka yi aiki mai kyau yadda duniya za ta kalla, kuma ta gamsu an yi aiki mai kyau, kuma ma su kallo su more kudin su. Amma duk da hakan za mu buga shi a DVD mu yada shi a kasuwa, saboda sakon da ya ke cikin fim din. Domin shi fim din ya na dauke da sakon matsalar Almajiranci, musamman a Arewa da kuma illar shaye-shaye da Matasa su ke fama da shi, saboda haka akwai darrusa ma su yawa a cikin fim din, wanda idan fim din ya fita za a san an zo da wani abu da zai sauya akalar masana'antar Kannywood, wannan ya sa tun wuri ba mu yi masa shiri na wasa ba". A cewar Isah A Isah.
Jarumi Isah A Isah ya kuma yaba da hadin kai da ya sa mu daga abokan sana'ar sa yan fim da su ka yi aiki tare har zuwa kammaluwar aikin. Sannan ya kuma yi fatan Allah ya kara bunkasa masana'antar fina-finai ta Kannywood.

Labarai masu kamanceceniya