Na tarar da harkar fim ba kamar yadda na ke zato ba - Amina San

blogger@northflix.ng 2020-09-10 12:44:45 Labarai


Duk da cewar harkar fim a yanzu ta samu kan ta a cikin wani yanayin da a ke ganin ta tasamma durkushewa, to sai dai ma su magana na cewa "Faduwar wani tashin wani". Domin kuwa a yanzu ne wa su daga cikin Sabbin jarumai su ke samun damar taka ta su rawar da har ya zamo a ke jin su kuma a ke ganin su.
Sabuwar jaruma Amina Sani, ta na daya daya cikin jarumai mata da a yanzu ne su ka fara haskawa a cikin masana'antar. Domin kuwa duk da ta samu kusan shekaru Uku a cikin harkar, jarumar ba a fara sanin ta ba sai a dan wannan lokacin, kuma bisa dukkan alamu nan gaba kadan za ta iya shiga sahun jarumai masu haskawa. Saboda yanayin kyakyawar kirar da kuma yadda ta ke da nutsuwa hakan zai ba ta damar samun nasarar da ta ke bukata ta harkar fim.
A lokacin da mu ka ji ta bakin jaruma, Amina Sani dangane da dalilin shigowar ta harkar fim. Jarumar ta yi mana bayani, tun daga tarihin rayuwar ta, inda ta fara da cewar. ”Ni ‘yar asalin jihar Taraba ce, amma an haife ni ne a garin Jos, kimanin shekaru 24 da su ka gabata, amma ban yi karatun boko mai nisa ba, sakamakon zaman Saudiyya da na yi na tsawon lokaci, amma dai na yi karatu na daidai gwargwado. Bayan tsawon lokaci da na yi na zama a Saudiyya, sai kuma na dawo gida da zama, inda kuma mu ka koma jihar mu ta asali Taraba tare da iyaye na. Bayan na dawo ne sakamakon sha'awar da na ke da ita da harkar fim ne ya sa a cikin shekarar 2017 na yanke shawarar shiga harkar fim, inda na hadu da Darakta Amir Iliyasu Maross, wanda a dalilin sa ne na samu kai na a matsayin jaruma”.
Da mu ka tambaye ta manufar ta na shiga harkar fim kuwa cewa ta yi. “Ni daman tun ina karama na ke da sha'awar shiga harkar fim, domin haka abu ne da na dade ina burin sa a cikin zuciya ta, saboda haka da na girma na mallaki hankali na sai na samu damar fara harkar bayan karfin gwiwa da na samu daga wajen iyaye na, kuma Alhamdulillahi, a yanzu na samu kai na a cikin harkar fim, harkar da na dade ina sha'awar na ganni a ciki".
Ko fina-finai nawa ki ka yi zuwa yanzu?
”A gaskiya na dan yi fina-finai da dan dama, musamman a kamfanin mai gida na Amir Enterprises, kuma daga cikin su akwai Tuggu, Makari, Mijin Hajiya, Kisan Boko da dai sauran su. Kuma na yi wakoki da dama wanda har yanzu ma ina kan yin su, wa su sun fito, wa su ba su fito ba".
Ya ki ka samu kan ki a cikin masana'antar fina-finai?
"Gaskiya na tarar da ita ba kamar yadda na ke zato ba, domin a yadda na zata idan na zo zan samu 'yan fim mutane ne ma su girman kai, amma da na zo sai na ga sabanin hakan, domin sun girmama ni babu wani da ya nuna mini wani abu da zai bata mini rai, domin haka na tarar da ita ba kamar yadda na ke zato ba".
Menene burin Amina Sani a masana'antar fina-finai ta Kannywood?
"Ni babban buri na bai wuce na zama babbar Jaruma a duniya, domin haka a yanzu ba ni da wani buri da ya wuce na zama babbar Jaruma, kuma ina sa ran buri na zai cika".
Ko me ya fi burge Amin Sani a cikin harkar fim?
"To gaskiya abun da ya fi burge ni dai bai wuce yadda sunan ka zai daukaka a ko ina ba, domin yanzu dan fim duk inda ya je sai ka ga a na kallon sa, kuma ya zama abun sha'awa, to ka ga wannan abun burgewa ne, ina jin dadin hakan sosai".
Da ya ke kin dan samu lokaci a cikin harkar, ko akwai wata matsala da ki ke hanga a cikin harkar?
“To ka san yadda harkar rayuwa ta ke ko ina ba a rasa matsala, amma dai abun da na lura shi ne, a yanzu shugabanin 'yan fim su na ta kokarin yin gyara a cikin masana'antar, domin haka ina ganin nan gaba kadan abubuwa za su canza kuma za a samu gyara”. Inji Amina Sani.
Jaruma Amina Sani ta kuma yi fatan alheri ga ubangidan ta a cikin harkar wato Darakta Amir Iliyasu Maross da kuma Babangida Bangis, domin a cewar ta duk wani abu da ta zama a harkar fim su ne su ka zame mata tsani.

Labarai masu kamanceceniya