T Y Shaba ya hasko Tauraron boye

[email protected] 2020-11-05 23:44:08 LabaraiFitaccen jarumi kuma Furodusa a masana'antar finafinai ta Kannywood T. Y Shaba, ya saka fito da wani Sabon salon fim wanda a ke ganin kamar ya zo da wani sabon salon da ba a saba da irin sa ba a cikin masana'antar ta Kannywood,. A 'yan kwanakinnan ne dai ya kammala aikin wani fim mai suna Tauraron boye,fim din da ya dauki hankali masu lura da al' amuran da su ke kaiwa da komowa a cikin masana'antar fina-finai ta Kannywood.
Ganin yadda fim din ya ja hankalin mutane ne ya sa muka ji ta bakin T Y Shaba, ko wanne irin sabon Salo ya zo da shi a cikin wannan fim din na sa na Tauraron boye?
In da ya fara da bayyana mana cewar "shi fim din Tauraron boye yana nuni ne da irin yadda yara masu kwazo su ke tasowa da basirar su da kwarewa yadda jama'a za su amfana, to Amma sai Ka ga iyaye sun dora su a kan wani ra'ayi na su wanda bai yi dai-dai da baiwar da suke da ita ba, sai ka ga ana yin kokarin a dora yara a kan wata Kwarewa ko wani tafarkin da kwakwalwar Yaron ba za ta iya dauka ba, daga karshe kuma za a iya samun sabani daga wajen Yaron ko kuma a samu Matsaloli wajen aikin da aka ce sai ya koya, don haka muka tsara labarin a kan wannan.
Ya Kara da cewar "za ka ji ana cewar 'ana zaton wuta a makera sai ta tashi a masaka, to za ka ga cewar akwai iyaye da dama da za ka ga mutum ya kai dan sa babbar makaranta yana kashe masa kudi sosai, saboda yana son ya samu ingantaccen ilimi, sai ka ji ya ce ni yaro na so na ke ya zama Likita, amma ba ya tunanin shinYaron yana da kwakwalwa da basirar ya zama likita? To ka ga Uban shi ne ka wai ya ke son dan sa ya zama likita ko ya zama lauya ko wani abu daban, amma bai yi tunanin ko Yaron ba shi da sha'awar da zai samu damar da zai yi karatun da zai zama abin da ya ke son ya zama ba, don haka ta yiwu shi Yaron akwai baiwar da Allah ya kimtsa masa a kwakwalwar sa wanda shi ne zai iya yi. To yana da kyau Uba tun daga farko wanne bangaren Yaron ya ke da karfi ta yadda za a taimaka masa domin ya kai ga cimma samun wannan abin, don haka Tauraron boye labari ne a kan wani yaro dan makarantar firamare da Uban sa ya ke da sha'awar zama shugaban Hukumar kula da shige da fice ko kuma lauya. Badon komai ba saboda Uban sa yana harka irin ta fasa kwauri, ta haka ne ya ke gani idan dan sa ya zama daya daga cikin biyun nan zai samu abin da ya ke nema na kariya daga haramtacciyar sana'ar sa,ta hanyar sa, amma dai shi Yaron Allah ya yi masa baiwa irin ta waka ne, amma a kokarin a jawo hankalin Uban a kan baiwar da dan sa ya ke dauke da ita duk wani bala'i ya faru. "
Fim din dai kamar yadda T Y Shaba ya bayyana mana yana da sarkakiyar gaske don haka ne ma hankalin jama'a ya tafi a kan sa. Kuma jarumai da dama na cikin masana'antar finafinai ta Kannywood da kuma na Nollywood sun taka rawa a ciki, wani Karin armashi da fim din ya ke dauke da shi ma har da jarumin Hollywood da kuma wani dan kasar Lebanese a ciki. Ana sa ran dai a karshen shekaran nan za a fara kallon fim din a manyan Sinimu na kasar nan da ma wasu daga cikin kasashen Africa.

Labarai masu kamanceceniya