An bayar da belin Naziru Sarkin Waka

[email protected] 2020-11-06 08:26:50 Labarai

 

Kotun majistrate da ke Noman's Land a jihar Kano ta bayar da belin mawaki Nazir M. Ahmad wanda a ka fi sani da Sarkin Waka.
Naziru Sarkin Waka ya shafe kwanaki biyu a gidan ajiya da gyaran hali, tun bayan da a ka tsare shi a kulle.
Lauyan Sarkin Waka, Barrister Sadik Sani Kurawa, ya bayyanawa manema labarai cewa” A yau Juma’a mu ka cika dukannin umarnin da Kotu ta bukata na bayar da beli, kuma yanzu haka Naziru Sarkin Waka ya fito daga gidan ajiya da gyaran hali na Kurmawa”. Inji Barrister Sadik.
Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ce ta shigar da karar a kan wa su wakoki guda biyu da ya fitar da su ba tare da izinin hukumar ba, wanda ya buga su tun a shekarar 2014. 
Za dai a ci gaba da sauraron shari’ar ne a ranar 1 ga watan Disambar wannan shekarar ta 2020.

Labarai masu kamanceceniya