SADIYA HARUNA ZA TA BAR WA YAYANTA ABUN KUNYA. -Mansura Isah

blogger@northflix.ng 2019-11-27 01:57:59 Labarai

A cikin karshen makon nan ne dai labari ya rika yawo kamar wutar bazara a soshiya midiya na   matashiyar nan wadda ta yi kaurin suna wajen sayar da kayan mata da kuma yin bidiyo na batsa a dandalin sada zumunta na Instagram mai suna Sadeeya Haruna.

Kwanaki kadan bayan da mai bada umarni a Kannywood Sunusi Oscar 442 ya yi mata wasu bidiyoyi na yabon Manzon Allah (S.A.W) aka daina ganin maganganun batsa a shafukanta, har ma wasu suka fara tunanin kila wakokin ne sanadiyyar shiryuwarta, sakamakon goge duk wani bidiyo da ta yi wanda ya nuna tsiraicin ta  da kuma canjin suna da ta yi daga Sadeeya Haruna zuwa "Sayyada Sadeeya Haruna" a shafin Instagram bayan an saki faifen bidiyon na ta na yabon Manzon (S.A.W). 

Kwatsam ba a fi sati guda ba, da tunanin tubar da ake ganin Sadeeya ta yi na daina shigar banza,  sai aka ga ta kara yin  bidiyon da ta wallafa a shafinta na Instagram.

A cikin bidiyon ta bayyana fitaccen jarumin Finafinan Hausa mai suna Isah A. Isah, a matsayin dan luwadi, sannan ta fito karara ta bayyana cewa sun taba auren mutu'a na wata uku da jarumin, har ma ta bugi gaba ta ce idan ya isa ya fito fili ya karyata maganganun da ta yi.

Masu sharhi akan al'amurran yau da kullum dai sun yi sharhi tare da yin tir gami da Allah wadai game da abun da suka aikata. Labarin bidiyon na ta ya yi yawo a sosai inda aka rika yada shi da taken "Yadda ake auren Mutu'a a Kannywood.”

Sai dai daga bangaren Isah A. Isah, bai fito fili ya karyata maganganun Sadiya ba, amma an ga ya yi bidiyo yana ba abokan sana'ar sa ('yan fim) hakuri bisa wani kuskure da ya yi, wanda bai bayyana ko mene ne ba, sai dai daga bisani ya goge bidiyon a shafin sa na Instagram.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Sadiya ta fara fada da 'yan Kannywood a Instagram ba. Ta yi fada mutane akalla za su kai 10 cikin su har da shugaban jarumai masana'antar Kannywood wato Alhassan Kwalle, wanda ta bayyana cewa ya taba neman ta da yin zina amma ta ki yarda. Ko da yake ya fito ya kare kan sa a wani dan guntun jawabi mai tsawon minti 6, wanda ya rika turawa mutane a WhatsApp. Sannan yasa 'yan sanda suka kulleta har ma ta bayyana cewa ita ba 'yar Kannywood ba ce. A wancan lokacin an zargi Isah A. Isah da daure mata gindi tare da kokarin yin belin ta.

Har sai da ta kai ga turka-turkar ta sanya tsohuwar jarumar Finafinan Hausa Matar Sani Musa Danja, wato Mansura Isah ta fito a Instagram ta yi tsokaci game da Sadiyar.

Har ma ta ce ba za ta iya sanya hoton ta ba, saboda dambarwar da ake ciki. Sannan ta gargade ta da cewa idan fa ba ta shafawa kan ta lafiya ba, za ta bar wa 'ya'yan ta abun kunya.

Ga dai abin da Mansura Isah ta rubuta game da takaddamar:  "Ba zan iya saka hoton ki ba ma a shafina na Instagram.

“Saboda Bana tausiyinki ko kadan wallahi, Ban kuma Damu dake ba ko kadan domin kin zubarwa da kanki mutunci.

Amma ki sani kin wulakanta kanki da na ’yayanki da zaki haifa nan gaba, duk abinda kika rubuta a social media ko kin goge bai gogu ba saboda ya riga ya tafi kuma baki isa ki goge ba ko shekara nawa zai yi.”

“Kin tonawa kawar ki da kanki asiri kije YouTube idan baki sani ba kiga yadda hotunan ki da bidiyo y'ayinki ke yawo.

Wanda kika zubarwa kanki mutunci, Bance ba zaki samu mijin aure ba saboda akwai Mutane masu Imani amma ki duba halin da zaki sa ya'yan da zaki Haifa.

Gwara mu fim muka yi kuma mun fita lafiya Amma duk da haka Hakan ya zama abin gori ga ya'yan mu ana masu gori da shagube a makaranta da wurare daban daban ana cewa iyayen su Yan fim ne, abin yana damuna Amma ba yanda zanyi. Inaga ke da kike fitowa kina wulakanta kanki ki gaggauta tuba Allah yana yafe ko wane irin laifi ki kuma gyara.”  In ji Mansurah.

Labarai masu kamanceceniya