KOTU TA GARKAME SADIYA HARUNA A KURKUKU

blogger@northflix.ng 2019-11-27 01:55:19 Labarai

Rahotanni sun bayyana cewar, a yau Laraba, 16 ga watan Oktoba 2019 wata  Kotun majistret mai lamba 15 karkashin mai sharia Muntari Garba Dandago ta aika da wata mata mai suna sadiya Haruna gidan yari. Kazalika tun da farko ‘yansanda ne suka gurfanar da ita bisa zargin bata suna, laifin da ya saba da sashi na 391 na kundin hukunta masu laifin Penal code.

A yayin zaman kotun mai shari'a Muntari Garba  ya karanto Kunshin tuhumar ya bayyana cewar wani mashiryin shirin Hausa kuma Jarumi a masana’antar Kannywood mai suna Isa A Isa shine yayi korafin akan cewa sadiyar ta bata masa suna.

A makon da ya gabata mun rawaito muku tsokacin abin da ya aukwu tsakanin ita Sadiyar da mijinta Isah A Isah wanda ta ce sun yi auren mutu’a da shi ba tare da saninta da kuma kiransa da wasu sunaye na batanci.

Wannan shi ya tunzira Mijin na ta har ya buga ta a kotu domin bin hakkinsa.

Labarai masu kamanceceniya