KO ME YASA MAISHADDA YAKE HADA MARYAM YAHAYA DA UMAR M SHAREEF A FIM?

[email protected] 2019-10-20 06:18:33 Labarai

A kokarin sa na rike kambun sa na zama fitaccen Furodusa a masana’antar Kannywood, Abubakar Maishadda ya karfafa alakar finafinan sa a kan Jarumai guda biyu, wato Maryam Yahaya da Umar M Shareef, inda ma’abota kallon finafinan Hausa ke korafi a kan yadda Maishaddan ke maimaita fuskokin Jaruman guda biyu a ma fi yawancin finafinan sa. A dalilin hakan ne wakilinmu ya tattauna da Furodusan akan haka.

“Dalilin da Yasa nake yawan hada fuskoki guda biyu Maryam Yahaya da Umar M Shareef shi ne tun a bayan lokacin da suka yi fim din da ya shara mai suna MANSOOR wanda shi ne fim dinsu na farko a matsayin jarumai wanda kamfanin Fkd Production suka shirya a karkashin jagorancin Ali Nuhu a shekara ta 2017. Mu ka sake hada su fim mai suna MARIYA a shekara ta 2018 wanda wakokin  fim din da fim din suka yi tashe na azo  a gani har ya kai ga ana hawa wakar fim din a wuraren taro da bukukuwa a shekarar da ta gabata, Bayan nan kuma mu ka sake hada su a finafinai kamar haka HAFEEZ, SAREENA, HALIMATUSSADIYA da Sauransu”.

Yawan hada su a fim ya jawo abin magana wajen yan kallo, Suna korafin cewa me yasa ake yawan hadasu fim. Ko me Za ka iya cewa akan hakan?

Furodusan ya amsa da cewar “indai fina finan suna  bada ma'ana kuma suna isar da sakonnin da ake so su isar yana ganin korafi ba matsala bane."Daga lokacin da aka kafa Kannywood zuwa yanzu zakuga bani  kadai Bane wanda nake yawan hada Jarumai biyu a fim, idan kuka kalla  zakuga ko wani kamfani akwai jaruman da suke jin dadin aiki dasu, ku kaddara duk labaran da nake dakkowa nake yi suna dace wa da Maryam Yahaya da Umar M Shareef kuma suna bada hadin kai dari bisa dari wajen tsaya wa ayi aiki mai kyau gaskiya ni hadin su yayi mun a fim." Inji Maishadda.Ya kuma Kara da cewa yana yiwa masoya kallon Finafinan Hausa albishir da Sabbabin fina finan da zai fara dauka nan ba da jimawa ba masu dauke da darussa da kuma tabarbarewar rayuwar Yara Yan Mata a yanzu da iyayen su, da kuma illar soshiyal midiya ga Yara mata a yanzu.

Daga karshe ya yiwa masoyansa godiya akan irin soyayya da kaunar da suke nuna masa.

Labarai masu kamanceceniya